Rahotannin daga jihar Benuwai a Arewa maso tsakiyar Nijeriya na bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da wani ɗalibin likitanci mai sanin makamar aiki a jihar da ke fama da matsalar ƴan bindiga.
An kai wa ɗaliban harin ne a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa Kudu maso Gabashin Jihar Enugu a ranar 15 ga watan domin halartar taron Ƙungiyar Ɗaliban Likitanci na shekara-shekara.
“Daliban, waɗanda aka ce ƴan Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Jos ne, suna tafiya ne a tare, inda ƴan bindigar suka afka musu da misalin ƙarfe 3:30 na yamma a yankin Otukpo na jihar.”
Kakakin Rundunar ‘Yan sanda, Catherine Anene, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Harkar garkuwa da mutane ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda lamarin ya fara zama ruwan dare a ƙasar ta Afirka ta Yamma.
A watan Mayu, ƴan bindiga sun kashe mutum 11, sannan suka sace wasu da ba a tantance adadinsu ba a Ƙaramar Hukumar Agatu ta Jihar Benue.
Haka kuma a Janairu, aƙalla fasinjoji guda 45 ne aka sace a lokacin da ƴan bindiga suka tare wasu motoci a kan hanyar Otukpo-Enugu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 26 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 7 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com