Hukumar dake lura da gidan ajiya da gyaran hali ta Calabar dake jihar cross river ta ce ta na bincike kan matsalar ciyar da daurarru dake ajje a gidan domin tabbatar da walwalar su.
Kakakin hukumar na jihar Abubakar Umar ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da kamfanin dillanci labarai na Nijeriya NAN a birnin Abuja ranar talata.
Inda yace ministan cikin gida na Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan zargin badakala a harkokin ciyar da daurarru a gidan ajiya da gyaran hali na Afokang dake tsakiyar Calabar a jihar Cross River.
Umarnin na zuwa ne bayan wani faifan bidiyo daya fito kan yadda ake lura da daurarrun, wanda ciki harda yadda ake basu wani wake da bai dahu ba a lokacin Karin kumallo.
Read Also:
Ko dai ta cikin wani sako da Dan jarida Ja’afar Ja’afar Ya wallafa a shafinsa na facebook ya bayyana yadda wani ma’aikacin gidan gyaran hali da tarbiyya ya aike masa da wani sako kan halin da daurarru ke ciki a gidan ajiya da gyaran hali.
Sakon yace “Sir mutane na mutuwa a Prison saboda yunwa” “Wallahi a inda nake aiki kullum sai an fita da gawa” “kuma Yunwa ce”.
“sun hana kowa shiga da Phone (waya) don kada a dauki hoton abinci”
“hoton dake yawo na calaba Prison to kusan duk sauran prison din haka suke babu abinci”
“Staff wani lokacin ke taimakon Inmate da abinci da ga cikin salary su” “wallahi ko ni kusan duk sati sai na sayi kuli-kuli da garin rogo na rabawa inmate”.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 27 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 8 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com