Jami’an NEMA sun fara kai agaji Maiduguri

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce ta fara kai agaji domin kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri, babban birnin jihar Borno; ambaliyar ta biyo bayan fashwar madatsar ruwa.

Wannan dai na cikin wata sanawar da babbar darektar hukumar Zubaida Umar ta fitar a shafinta na X, ta ce sun kuma fara shirye-shiryen tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa da abinci, matsuguni da kuma magaunguna.

Yankunan da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Shehuri, rukunin gidaje da ke G.R.A, Gambomi, Budum, Bulabulin, Adamkolo, Millionaires Quarters, kasuwar Monday Market da kuma Gwange.

NEMA ta ce gwamnatin jihar Borno ta buɗe sansanin Bakassi domin tsugunar da mutanen da ambaliyar ta shafa.

Ta ce suna aiki da hukumar ba da agaji reshen jihar ta Borno domin tallafa wa mutanen da ke cikin sansanin.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 30 minutes 31 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 11 minutes 56 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com