Home General Atiku ya yi martani kan kalaman Akume ga ‘yan Arewa

Atiku ya yi martani kan kalaman Akume ga ‘yan Arewa

Wasu kalamai da suka fito daga bakin sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume, na neman ‘yan siyasar arewacin ƙasar su jira har shekarar 2031 idan suna son yin takarar shugabancin ƙasar, sun janyo cece-kuce.

Mista Akume, ya faɗi hakan ne yayin hira da wani gidan talabijin a ƙasar, inda ya ce kamata ya yi a bar yankin kudancin Najeriya ya karasa shekaru takwas ɗin sa, kamar yadda itama Arewa ta yi lokacin mulkin shugaba Buhari.

Kalaman dai sun girgiza ƴan siyasar arewacin Najeriya, inda tuni aka fara mayar da martani.

Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Abdulrashid Shehu Uba, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowaye damar fita don neman kujerar shugaban ƙasa.

“Babu wata yarjejeniya da aka yi ko kuma aka yadda za a tafi a kan wannan tsari. Idan su a APC sun yi wannan tsari mu ba haka yake a wajenmu ba. Ya kamata su tsaya su mayar da hankali kan zaɓen da suka ƙwace,” in ji Abdulrashid.

Kakakin na Atiku ya ce kowa na ganin yadda al’amura suka taɓarɓare a yanzu musammman ɓangaren tsaro da kuma tsadar rayuwa, inda ya ce da gwamantin APC ta yi aiki ba za ta fito ta ce kada wani ya yi takara ba.

Ya ce babu wani ɗan siyasa da suke tsoro kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp