Home General Mene ya sa Gwamnonin Nijeriya ke butar ýan sandan Jiha

Mene ya sa Gwamnonin Nijeriya ke butar ýan sandan Jiha

Majalisar tattalin arzikin Najeriya (NEC) ta karɓi rahotonnin matsayar gwamnonin jihohin ƙasar 36 kan kafa rundunonin ‘yansandan jihohi.

Majalisar tattalin arzikin ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, ta yi zamanta a jiya Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, inda gwamnoni da mataimakan wasu gwamnonin suka halarta tare da wasu masu bai wa shugaban ƙasa shawara.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jim kaɗan bayan kammala ganawar, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce gwamnonin jihohin sun nuna cikakken goyon bayansu kan ƙirƙirar ‘yansandan jihohi saboda matsalolin tsaro da jihohin ke fama da su.

“Tabbas kowace jiha na da irin nata matsalolin da suka shafi tsaro, kuma da dama sun amince da kafa rundunonin ‘yansandan jihohi a matsayin mafita kan matsalolin,” in ji gwamnan na Kaduna.

To sai da majalisar ta dakatar da tattaunawa game da batun har sai a zamanta na gaba da za a yi cikin watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp