Home General ‘Ƴansanda sun kama mutum fiye da dubu 30 tare da ƙwato makamai...

‘Ƴansanda sun kama mutum fiye da dubu 30 tare da ƙwato makamai a 2024

Babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya ce jami’an rundunar sun kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban har mutum 30,313, sannan sun ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar 2024.

Shugaban ƴansandan ya bayyana haka ne a taron ganawa manema labarai a ranar Talata, 24 ga watan Disamba a Abuja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce sun bayyana nasarar da suka samu ne domin nuna irin shirin fuskantar baɗi da suke yi.

Shugaban ƴansandan ya yaba da ƙokarin jami’ansa da sadaukarwar da suka yi a shekarar, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar ce tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, inda ya ƙara da cewa ana buƙatar hakan domin tabbatar da tsaro mai inganci.

“Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar daƙile masu aikata laifuka, inda ta samu nasarar kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban guda 30,313 da ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250, sannan mun ceci waɗanda aka yi garkuwa da su guda 1,581.”

Ya kuma yi kira ga hafsoshin rundunar su riƙa amfani da kimiyyar zamani domin aikinsu ya ƙara nagarta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp