Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar kasar na sabuwar shekara, kalaman baka ne kawai.
A jawabin da Tinubun ya yi ranar Laraba 1 ga watan Janairun, 2025, ya bayyana tsare-tsaren da ya ce gwamnatinsa za ta bullo da su domin rage tsadar farashin abinci da samar da tsaro da kuma wasu nasarori da ya ce gwamnatinsa ta samu.
Ya ce duk abubuwan da Tinubun ya fada na cewa gwamnatinsa ta samu nasara, kamata ya yi a ce an gan su a fili muraran, kamar yadda akan ce, ”an ce da kare ana biki a gidanku ya ce to mu gani a kasa.”
Tsauri ya ce duk abubuwan da ya fada ba a takarda ya kamata a gan su ba, yana mai nuni da cewa idan har gaskiya ne gwamnatin ta samu wannan nasara da Tinubun ya fada to jama’a su gani amma lamartin sabanin haka yake.
”Ba abin mamaki ba ne in Shugaban Kasa ya yi wadannan maganganu domin kawai ya sanar da ‘yan Najeriya ba don ya dadada masu ba, don duk abin da ya fadi kowa ya sani ba za a ce karya ba ne amma ba gaskiya ba ne – misali in an ce mana farashin mai ya ragu yaushe ya ragu?” In ji shi.
Ya ce gwamnati na cewa farashin dala ya ragu naira ta kara samun daraja, to amma ya yi nuni da cewa, ” mun wayi gari dala ta koma naira 1600 daga naira 1700, cewa ake an samu nasara, to wace nasara aka samu bayan lokacin da Buhari ya hau mulki muna sayen dala naira tamanin?”
”To wane irin cigaba ne wannan? Mu a wurinmu Turanci ne aka rubuta kuma ya karantu,” in ji shi.
A dangane da kalaman shugaban ne jam’iyyar PDP ta bakin tsohon sakatarenta na kasa Sanata Umaru Tsauri, ta mayar da martani da cewa kalaman soki-burutsu ne kawai.
A tattaunawarsa da BBC, Tsauri ya ce, abubuwan da shugaban ya karanta abin da su suka dauka an rubuta masa Turanci ne kawai ya karanta, amma ba wai abubuwa ne da suke a zahirin gaskiya ba.
Ya ce duk abubuwan da Tinubun ya fada na cewa gwamnatinsa ta samu nasara, kamata ya yi a ce an gan su a fili muraran, kamar yadda akan ce, ”an ce da kare ana biki a gidanku ya ce to mu gani a kasa.”
Tsauri ya ce duk abubuwan da ya fada ba a takarda ya kamata a gan su ba, yana mai nuni da cewa idan har gaskiya ne gwamnatin ta samu wannan nasara da Tinubun ya fada to jama’a su gani amma lamartin sabanin haka yake.
”Ba abin mamaki ba ne in Shugaban Kasa ya yi wadannan maganganu domin kawai ya sanar da ‘yan Najeriya ba don ya dadada masu ba, don duk abin da ya fadi kowa ya sani ba za a ce karya ba ne amma ba gaskiya ba ne – misali in an ce mana farashin mai ya ragu yaushe ya ragu?” In ji shi.
Ya ce gwamnati na cewa farashin dala ya ragu naira ta kara samun daraja, to amma ya yi nuni da cewa, ” mun wayi gari dala ta koma naira 1600 daga naira 1700, cewa ake an samu nasara, to wace nasara aka samu bayan lokacin da Buhari ya hau mulki muna sayen dala naira tamanin?”
”To wane irin cigaba ne wannan? Mu a wurinmu Turanci ne aka rubuta kuma ya karantu,” in ji shi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 18 hours 44 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 20 hours 25 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com