Home General Sojojin saman Nijeriya sun hallaka Dan Ta’adda Rusu da mayakansa a jihar...

Sojojin saman Nijeriya sun hallaka Dan Ta’adda Rusu da mayakansa a jihar Zamfara

Dakarun sojojin saman Nijeriya karkashin Operation Fansan Yamma sun sami nasarar hallaka dan bindigar nan Sani Rusu, a wani hari da ta kai kauye Bamamu dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Kodinatan cibiyar hadin gwiwa ta yada labaran dakarun Operation FANSAN YAMMA Abubakar Abdullahi ya aikewa PRNigeria a safiyar litinin 6 ga watan Janairu 2025.

Sanarwa ta ce yayin yarin saman da dakrun suka kai maboyar dan Ta’addan sun yi misayar wuta da mayakan dan bindiga inda suka sami nasarar tarwatsasu tare da hallaka Rusu dake addabar al’ummar yankin.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa a ranar 4 ga watan janairu dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kai wani harin kwantan bauna, wanda ya basu nasarar dakile ayyukan taddanci a kwanar Jollo dake karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, in da suka sami nasarar hallaka ‘yan ta’adda tare da samun damar kwato tarin makamai da suka hadar da bindiga kirar AK47 bindiga kirar G3, hadi da zageyen alburusa masu tsayin 7.62mm na musamman da kuma wasu alburusan kirar NATO masu tsayin 7.62mm da babu hawa guda 3

Abubakar Abdullahi  ya kara da cewa dakarun Operation FANSAN YAMMA sun gudanar da wani hari ta sama a tsakanin Fakai da Kware a karamar hukumar ta shinkafi a ranar 30 ga watan disambar shekarar da ta gabata.

Wannan hari ya auku ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addan na karkashin jagorancin dan ta’addan nan Bello Turji yayin da suke tsaka da ganawar sirri a yankin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp