Home General Arewa Na Da Hanyoyin Tara Haraji Daga VAT Da Dama – CNG

Arewa Na Da Hanyoyin Tara Haraji Daga VAT Da Dama – CNG

Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya CNG, ta ce yankin arewa na da dimbin hanyoyin tara harajin da za su cike gurbin kudurin dokar sabunta haraji da ke gaban majalisar dattawa.

Wannan ya biyo bayan zama da kwararru kan hanyoyin raya tattalin arziki, da kungiyar ta yi a Abuja don neman mafita idan kudurin ya samu nasara.

CNG wacce ta sake nanata bukatar dakatar da kudurin don yi ma sa garambawul da zai dace da muradun kowane yanki, ta ce hakkin ya rataya a kan ‘yan Arewa a majalisa su tabbatar ba’a yi wa yankin sakiyar da ba ruwa ba.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Jamilu Aliyu Charanci ya ce arewa ka iya samun dimbin kudin shiga daga albarkatun noma da kiwo matukar aka tabbatar ana karbar haraji kan duk buhun abinci da za’a fitar daga arewa a kuma daina kai shanu kai tsaye kudu maimakon haka a rika yankawa a na tura naman.

Wannan matsaya ta zo dai-dai da hangen tsohon sakataren gwamnati Mista Babachir David Lawan, wanda ya yi misali da arzikin noma da kiwo na jihar Adamawa “an tare ka an kirga shanu a ka ce kowace saniya ka biya haraji Naira dubu biyar, na yi lissafi a shekara ba za mu gaza samun akalla Naira Bilyan kusan dari ba. A na zuwa Mubi a na siyan shanu 300,000-400,000 to in ka kara N5000 a kai ya yi wani abu ne?”

A karshe Jamilu Charanci ya yi hannunka mai sanda ga ‘yan majalisar “al’umma su tashi su rike ‘yan majalisar su gam, wannan kudurin idan ya tsallake ba wadanda su ka cuce mu sai ‘yan majalisar mu, idan kuma a ka maido shi a ka janye shi to ku sani ba wanda ya taimake mu sai ‘yan majalisar mu”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp