Home General Kotun Ƙoli ta amince da ɓangaren Wike na majalisar jihar Rivers

Kotun Ƙoli ta amince da ɓangaren Wike na majalisar jihar Rivers

Kotun Ƙolin Najeriya ta umarci babban akanta da babban bankin ƙasar wato CBN na Najeriya da su dakatar da kason kuɗin jihar Rivers, har sai gwamnan jihar ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban halastacciyar majalisar jihar.

Alƙalan kotun su biyar ne suka yanke wannan hukuncin, inda kotun ta ce Martins Amaewhule ne sahihin shugaban majajlisar.

Wannan ya kawo ƙarshen lokaci mai tsawo da aka ɗauka ana shari’a tsakanin ɓangarorin biyu kan rikita-rikitar siyasa a jihar.

Haka kuma ana ganin wannan matakin a matsayin wata nasara ga ɓangaren Ministan Abuja, Nyesome Wike, kan Gwamnan jihar, Sim Fubara.

Mai shari’a Emmanuel Agim ne ya karanta hukuncin, inda ya ce, “muna umartar Babban Bankin Najeriya CBN da Babban Akanta na Najeriya da su dakata da tura kuɗin kason jihar Rivers har sai gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban majalisar jihar ƙarƙashin Martin Amaewhule,” kamar yadda ya bayyana.

A gefe guda kuma, a wata shari’ar daban, kotun ƙolin ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka yi a ranar 5 ga Oktoban 2024.

Mai shari’a Jamilu Tukur, ya ce zaɓen wanda hukumar zaɓen Rivers mai zaman kanta ta shirya, ya saɓa da sashe na 150 na kundin tsarin zaɓe na ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp