Home General Alhaji Aminu Ado Bayero ya dakatar da hawan Karamar sallah a Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero ya dakatar da hawan Karamar sallah a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya dakatar da tsarin bikin hawan sallah karama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu.

Ya ce bayan samun shawarwari da kiraye kiraye daga shugabanni da iyaye da Malamai da kuma tattaunawa da yan Majalisar Sarki ya zama wajibi a dakatar da hawan Sallah Karama na wannan shekara.

Sarkin ya ce Hawan Sallah ba abune na ko a mutu ko ayi rai ba, Wanda idan yin hakan zai kawo tashin hankali ko hargitsi da kawo rashin zaman lafiya to ya zama wajibi a hakura dayin hawan.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce a matsayinsa na Sarkin Kano ya dauki alkawarin kiyaye Imani da mutunci da dukiya da zaman lafiyar al’umma Wanda hakan ce ta sa ya ga dacewar daukar wannan mataki domin kaucewa dukkan wani abu daka iya kawo tashin hankali ko rashin samun zaman lafiya a tsakanin al’umma.

A don haka ne Mai Martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da sauran masoya su yi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin samun dorewar zaman lafiya a jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Sarkin na Kano ya yi amfani da wannan dama wajan kira ga al’umma da su yi amfani da lokutan bukukuwan Sallah wajan ziyartar juna domin sada zumunci, inda ya taya al’umar musulmi murna da farin cikin gudanar da azumin watan Ramadan ya na mai addu’ar samu dacewar Ubangiji daga cikin bayinsa wadanda Allah yake gafartawa dayin rahama tareda karbar ibadar da aka gudanar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp