Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce za ta hukunta jami’anta da aka nuna suna ƙarbar kuɗaɗe daga hannun wasu ƴan ƙasar China a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
A cikin bidiyon, an ga wasu ƴan ƙasar China suna rabawa wasu jerin jami’an ƴansanda kuɗi, lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda ƴan Najeriya da dama ke nuna rashin jin daɗinsu tare da yin kira da a kawo sauyi kan yadda rundunar ke gundanar da ayyukanta.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar ƴansandan na dandalin X, kakakin rundunar Muyiwa Adejobi, ya yi Allah-wadai da halin jami’an, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin rashin da’a.
Ya ce, “Halayyar waɗannan jami’an ta saɓawa ƙa’idojin da’a, da muhimman dabi’u na rundunar ƴansandan Najeriya.”
Ya ƙara da cewa rundunar ta zuƙulo jami’an da lamarin ya shafa kuma ana shirin ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.
Ko da yake bai bayyana yanayin matakan da za a ɗauka kan ƴansanda ba, Adejobi ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.
Rundunar ta kuma gargadi mutane da ƙungiyoyi masu amfani da ƴansanda, a matsayin masu rakiya da masu gadi da su kaucewa duk wani aiki da zai iya zubar da mutuncin jami’anta ko kuma janyo wa rundunar bacin suna.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 8 hours 44 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 10 hours 25 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com