Home General Gwamnati ta gaza kare al’ummar jihar Zamfara – Amnesty

Gwamnati ta gaza kare al’ummar jihar Zamfara – Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta ce gwamnatin ƙasar ta gaza wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a, la’akari da yadda ƴan bindiga ke kashe mutane a jihar Zamfara ba tare da ƙauƙautawa ba.

Daraktan Ƙungiyar Malam Isa Sanusi wanda ke tsokaci akan kazamin harin da ƴan bindiga suka kai yankin Ɗangulbi dake ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara, suka kuma hallaka mutane 26, yace gwamnatin ba wai ta gaza ne saboda rashin jami’an tsaro ko kuma kudin da za’ayi aikin tabbatar da tsaro ba, sai dai saboda san rai da nuna rashin kula da rayuwar jama’a da kuma mayar da hankali akan siyasa.

Sanusi ya ce Najeriya na da isassun kuɗin da za’a sayawa sojoji duk abinda suke buƙata domin murkushe waɗannna yan bindiga da suka hana jama’a zaman lafiya a jihohin Zamfara da Kebbi da Sokoto da Neja da kuma Kaduna, amma saboda rashin mayar da hankali akan lamarin, ga shi an ɗauki dogon lokaci ana kashe mutane ba tare da magance matsalar ba.

Daraktan ya ce abinda ya faru a ranar alhamis ya daɗa jefa tsoro da kuma fargaba a tsakanin mutanen Ɗangulbi, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici da ya afka akan jama’a.

Sanusi ya ce waɗannan ƴan bindiga sun dade suna ɗora haraji akan manoma da yan kasuwa a garuruwa, yayin da waɗanda suka ki biya kuma su gamu da fushin su ta hanyar kisa da kuma azabtarwa.

Daraktan ya ce mutanen wannan yanki na cikin yanayin bala’i, ta inda zuwa wasu wurare ma baya yiwuwa, sai mako mako idan sojoji sun raka matafiya, kafin su samu maslaha.

Satar dukiya da fyade ga mata da ‘ƴan mata ya zama ruwan dare, in ji shi, yayin da gwamnati ta kasa ɗaukar matakan da suka dace domin sauke nauyin da ya rataya akan ta, abinda ya sa wasu daga cikin waɗannan mutane ke cewa ba su san amfanin gwamnati a gare su ba.

A karshe, Sanusi ya ce gwamnati ta gaza domin ba zata iya kare lafiyar jama’a ba, inda ya ƙara da cewa a shekarar 2018 ya ziyarci waɗannan yankuna kuma ya ga abinda ke faruwa, kuma har ya zuwa yau babu wani abinda ya sauya daga irin ukubar da suke sha daga hannun irin waɗannan mutane.

Daraktan ya ce duk da ikrarin ɗaukar sabbin matakai na gwamnati, ya tabbata cewar waɗannan mataki basa aiki, saboda haka ya zama wajibi a zauna a tsakanin hukumomi da mutane domin nazari akan abinda ya dace, koda kuwa ɗauko sojojin haya ne ko taimako daga ƙasashen ƙetare.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp