Home General Dakta Abubakar Tanko Bala ya zama sabon shugaban Shirin nan na...

Dakta Abubakar Tanko Bala ya zama sabon shugaban Shirin nan na “Gas-by-Rail Freight Corridors Initiative” a Nijeriya

Sabon Ko-odinatan shirin nan Shirin nan “Gas-by-Rail Freight Corridors Initiative” na Najeriya, Dakta Abubakar Tanko Bala, ya yi alkawarin yin amfani da sabon mukamin nasa wajen ciyar da Najeriya gaba.

Dakta Abubakar ya bayyana hakan ne jim kadan da amsar takardar nadin mukamin nasa, wadda babban jami’in dake kula da shirin a fadin Duniya, Ambasada Musa Ibrahim Kuchi, ya sanya wa hannu, har kuma aka turawa Ko-odinatan shirin na Afirka ta yamma, Kabir Ishaq Sa’id Kwafin ta.

Dakta Tanko dai zai jagoranci masu ruwa da tsakin shirin a fadin Najeriya, wanda yake hadin gwiwa da ofishin majalisar dinkin Duniya, (United Nations Global Compact da Insight Dynamic Resources Ltd).

Manufar shirin shine domin samar da titin jirgin kasa me girman Kilo Mita dubu 70 a tsakanin kasashe 40 na Sahara dake nahiyar Afirka daga nan zuwa shekarar 2035, ta yadda zai bada damar taimaka wa al’umma wajen inganta harkokin sufuri da cinikayya a yankin Sahara na nahiyar Afirka

Haka kuma zai taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin, kare muhalli, inganta harkokin sufuri, la’akari da yadda za’a samar da guraben aiyukan yi kimanin Milyan 170 daga nan zuwa shekarar 2050.

A karshe ya buƙaci al’ummar kasar su taya shi da addu’ar Allah ya bashi ikon kawo canji mai ma’ana, ta yadda zai bada tasa gudunmawar wajen samar da kyakykyawar makoma ga kasar dama mutanen ta gaba-daya.

Dakta Abubakar Tanko Bala, dai ya kasance Sakatare Janar na Cibiyar nan ta shirya gasa a nahiyar Afirka, (Pan African Competitibeness Forum (PACF) reshen Najeriya, haka kuma shine ma’ajin kungiyar masu kanana da matsakaitan masana’antu na (NASSI) na Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp