Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan bada jimawa ba al’umma Najeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar.
Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, a lokacin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa ta dala biliyan 20, da ke yankin Lekki a jihar Lagos.
Ya ce sauyin da al’umma za su gani a yanzu, ba wai na rage farashin man ba ne, wanda zai sauya baki ɗaya yadda ake gudanar da harkokin mai ne a ƙasar.
Read Also:
A yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarcemu, kuma ya bamu ƙarin makamashi, ina mai sheda muku cewa nan bada jimawa ba za ku ji daga garemu, kuma zai kasance sauyi ne a ɓangaren mai baki ɗaya a ƙasar, ba wai kawai rage farashinsa ba ka ɗai.
A watan Oktoban bara ne dai matatar man Dangote ta fara saida man fetur, lamarin da ya kawo saukar farashinsa a Najeriya.
To sai dai dillalan man fetur a Najeriya, na ganin ya kamata matatar Dangoten ta rinƙa saida lita ɗaya ƙasa da Naira ɗari 8, la’akari da cewar ana sayar wa kamfanin ne da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon dalar Amurka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 13 hours 38 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 15 hours 19 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com