Wani rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce ana fuskantar tsaiko a tattaunawar da ake yi tsakanin Najeriya da kamfanin man fetur mafi girma a duniya mallakin Saudiya wato Aramco, dangane da shirin karɓar rancen Dala biliyan 5 da Najeriyar za ta biya da ɗanyen manta.
Wasu majiyoyi huɗu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faɗuwar baya bayan nan da farashin ɗanyen mai yayi a kasuwannin duniya shi ne ya janyo tsaikon, bayan da bankunan da ake sa ran za su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar suka bayyana damuwa kan sauyin farashin da aka samu.
Wasu alƙaluma dai sun nuna faɗuwar farashin ɗanyen mai nau’in Brent da kashi 20 cikin 100, inda ya koma Dala 65 daga Dala 82 a cikin watan Janairun da ya gabata, abinda ke nufin idan har ba za a fasa ƙulla yarjejeniyar karɓar rancen na Dala biliyan 5 ɗin ba, to fa dole Najeriya ta ƙara yawan gungunan ɗanyen man da za ta yi amfani da su wajen biyan bashin.
Read Also:
Biyu daga cikin majiyoyin da suka zanta Reuters, sun ce an fara tattaunawa kan shirin karɓar rancen ne a watan Nuwamban da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gadon Sarautar Saudiya Muhd Bin salman a yayin taron tattalin arziƙin da aka yi tsakanin Saudiyan da ƙasashen Afrika. Sai dai tun babu wani ƙarin bayani da aka taɓa bayyanawa kan neman bashin da Najeriyar ke yi, in banda yanzu da kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya ruwaito.
Idan za a iya tunawa cikin watan Mayu, shugaba Tinubu ya nemi amincewar ‘yan Majlisar ƙasar kan buƙatar gwamnati ta karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙasashen ƙetare, wanda kuma a ciki ne Najeriyar ke neman rancen na dala biliyan 5 daga kamfanin Man Saudiya na Aramco.
Ya zuwa yanzu dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai gano manyan bankunan da za su taimaka wajen aiwatar da wannan yarjejeniya ba, sai dai majiyoyinsa sun shaida masa cewar akwai guda daga nahiyar Afrika, yayin da ragowar za su kasance daga Yankin Gabas ta Tsakiya.
Idan har wannan yarjejeniyar karɓar bashin ta ƙullu, za ta kasance mafi girma irinta da Najeriya ta shiga, kuma karo na farko kenan da irin hulɗar ke shiga tsakanin Najeriyar da Saudiya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1461 days 22 hours 28 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 9 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com