Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasar da misalin ƙarfe 7 na safe a ranar Alhamis domin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2025.

Cikin wata sanarwa da kwamitin shirya bikin ranar Dimokradiyyar ya fitar, ya ce da rana kuma Tinubu zai halarci zaman haɗin gwiwa da ƴan majalisar dokokin ƙasar.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ba za a gudanar da taron faretin ranar ba a bana. A maimakon haka, za a gudanar da muhawarar jama’a a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ƙarfe 4 na yamma.

Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cika shekara 26 ƙarƙashin mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba tun bayan kawo ƙarshen mulkin soja a 1999.

A baya ana bikin ranar dimokradiyya a ranar 29 ga Mayu, wadda ke zama ranar rantsar da shugabannin ƙasa da gwamnoni da kuma ƴan majalisar tarayya da na jihohi.

Amma daga shekarar 2018, an sauya ranar zuwa 12 ga Yuni domin girmama zaɓukan 1993 da aka soke – da MKO Abiola ya lashe – zaɓen da ake ganin mafi sahihanci a tarihin Najeriya.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1461 days 21 hours 19 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1443 days 23 hours 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com