Home General DR Congo da Rwanda sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

DR Congo da Rwanda sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƙasar Rwanda sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya da nufin kawo ƙarshen rikicin da ke ci gaba da ɗaukar hankula a gabashin DRC, wanda ke da arzikin ma’adinai.

Ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu ne za su rattaba hannu a yarjejeniyar wadda Amurka ta shiga tsakani don warware rikicin, a mako mai zuwa, ranar 27 ga Yuni.

Yarjejeniyar na da nufin a ƙwace makaman mayaƙa, da kuma dawo da damar agajin jin ƙai ga al’umma a yankin da rikicin ya addaba.

Yarjejeniyar ta ƙunshi sharuɗɗa masu muhimmanci kamar girmama cikakken ikon ƙasa da iyakokin juna da haramta ci gaba da faɗa da Janyewar mayaƙa daga yankunan da suka mamaye da ƙwace makamai da kuma taimakawa wajen dawo da ‘yan gudun hijira da waɗanda rikicin ya raba da muhallansu

Tun farkon shekarar nan ne mayaƙan M23 suka ƙwace manyan birane biyu mafi muhimmanci a gabashin DR Congo.

DR Congo ta zargi Rwanda da bayar da tallafi da makamai ga mayaƙan, amma Rwanda ta musanta hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp