Home General Sama da mutane 40 ne aka kashe a wani hari da aka...

Sama da mutane 40 ne aka kashe a wani hari da aka kai asibiti a Sudan

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce sama da mutane 40 ciki harda ƙananan yara da kuma ma’aikatan kiwon lafiya ne aka kashe a wani hari da aka kai a wani asibiti da ke Sudan a ƙarshen mako.

Ofishin hukumar ta WHO da ke Sudan, ya ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai yara 6 da jami’an kiwon lafiya 5, sannan kuma anyiwa ginin asibitin mummunar ɓarna.

An dai kai harin ne kan Asibitin Al Mujlad da ke a yammacin Kordofan a ranar asabar da ta gabata, kusa da inda ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, a yaƙi da suke yi tun a watan Afrilun shekarar 2023.

Shugaban na WHO ya nemi a dakatar da kai wa ci biyoyin kiwon lafiya hari, duk da cewa bai ambaci sunan ɓangaren da ake zargi da kai wannan hari ba.

Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun zargi wani jigin yaƙin sojojin Sudan marar matuƙi da kai wannan hari, da wata sanarwa da aka fitar a ƙarshen mako ta ce mutunen da suka mutu sun kai 9.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp