Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa jami’anta sun karɓe iko da hedikwatar jam’iyyar PDP ta Wadata Plaza a ranar Litinin.
Rundunar ta ce tana son “ta nuna cewa babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al’amarin yake ba. An kai jami’an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
A wata sanarwa, rundunar ta ce “babu wani lokaci da jami’an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam’iyyar ta PDP.”
A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen watsa labarai da su yi kaffa-kaffa wajen tantance labarai kafin su wallafa shi.