Home Labarai Matatar Dangote ta rage farashin Man fetur

Matatar Dangote ta rage farashin Man fetur

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur daga Naira 880 zuwa N840 kowace lita.

Kakakin Rukunin kamfanoni Dangote, Anthony Chiejina, ya tabbatar wa da jaridar PUNCH cewa an rage farashin a daren ranar Litinin.

Ya ce sabon farashin ya fara aiki ne a ranar 30 ga watan Yuni.

“An rage farashin man daga N880 zuwa N840 kowace lita daga 30 ga watan Yuni,” Chiejina

Idan za a iya tunawa matatar man Dangote ta kara farashin man fetur zuwa naira 880 a daidai lokacin da rikici ya barke tsakanin Isra’ila da Iran na tsawon kwanaki 12, lamarin da ya sa farashin danyen mai ya Karye akan dala 80 kan kowacce ganga.

jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan kasuwar sun yi hasashen za a iya kara farashin daga ranar Litinin.

Abokan huldar matatar Dangote irinsu MRS, Heyden da AP ana sa ran za su rage farashin na su nan ba da jimawa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp