Lukurawa sun kashe mutum 15 a Sokoto

Rahotanni na bayyana cewa wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.

Ana zargin harin martani ne bayan kashe wasu mutum uku daga cikin kungiyar, ciki har da wanda ake zargin shugabansu ne a wani harin da ya ci tura da suka kai a baya a garin.

Ɗaya daga cikin shugaba a yakin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun dira ƙauyen ne a daidai lokacin da jama’a ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

“Muna cikin masallaci lokacin da suka kawo hari da yawansu.

“Da zuwansu suka fara harbe-harbe.” inji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba don halartar jana’izar waɗanda aka kashe.

“Wannan shi ne karo na farko da ƴan Lakurawa suka kai hari kai tsaye a garinmu.

“Amma ina ganin martani ne bayan kashe wasu daga cikin su a wani harin da ya faru a baya,” inji shi.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa ya ce maharan sun ƙone gonaki da gidaje da dama tare da lalata wata ariya ta sadarwa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1483 days 1 hour 47 minutes 49 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1465 days 3 hours 29 minutes 14 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com