Sojojin Najeriya sun kashe ƴan Bindiga fiye da 100 a jihar Neja

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai waɗanda ake kira bijilanti sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga biyo bayan wata fafatawa da suka yi  a tsakaninsu a ƙauyen Warari da ke Jihar Neja.

Rundunar ta ce artabun dai ya faru ne a ranar Talata wanda ta sami nasarar hallakafiye da ‘yan bindiga 100 waɗanda ke gilmawa a kan babura.

Lamarin ya faru ne bayan wani bayanin sirri da dakrun suka samu daga mazauna yankin game da hanyoyin da ‘yan bindiga ke bi don satar shanu.

Wannan ne ya bai wa sojojin damar kitsa kwanton-ɓauna da ya kai ga fafatawar da ta kai ga hallaka ƴan bindigan da dama.

wata shaidu sun tabbatarwa da PRNigeria cewa sojojin sun yi amfani da motoci masu sulke da makamai na zamani wanda ya ba su galaba a kan ‘yan bindigar.

Shugabannin al’umma a Warari sun tabbatar da girman rashin da ‘yan bindigar suka tafka, inda suka bayyana cewa gawarwakin wasu daga cikin su sun bazu a tituna da gonaki da dazuka da ke kewaye da yankin.

Neja na cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1498 days 12 hours 34 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1480 days 14 hours 15 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com