Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa da tsare tsohon gwamnan, lamarin da ta ce jam’iyyar APC ce ke neman jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin ruɗani.
A wata sanarwa sakataren watsa labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar, ya ce wannan na cikin yunƙurin cin zarafi da murƙushe jam’iyyun adawa a ƙasar.
Ya ce ana wannan kame-kamen ne “a daidai lokacin da aka fara ƙoƙarin samar da haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa kamen ba zai hana komai ba wajen yunƙurin da suke yi na kawo sauyi ba.
“Jam’iyyarmu na kira ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta daina zama karen farauta domin cin zarafin jam’iyyun adawa.
Tun da farko, Hukumar EFCC ce ta kama tare da tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi.
Rahotanni sun ce sanatan ya isa ofishin hukumar ne da kansa domin amsa gayyatar da aika masa a ranar Litinin, sannan ta riƙe shi.