Najeriya da Turkiyya za su ƙarfafa alaƙa a ziyarar da Tinubu ke yi a ƙasar

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu kekkyawar tarba daga takwaransa na Turkiya Recep Tayib Erdogan, bayan sauƙarsa jiya a Ankara, a wata ziyarar aiki da nufin ƙarfafa alakar ƙasashen biyu, sai dai ɗan tuntuɓen da shugaban ya yi a lokacin da ake masa faretin ban girma ya haifar da cece-kuce a Najeriya.

A ziyarar wadda ita ce ta farko zuwa Turkiya tun bayan ɗarewarsa shugabancin Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya ce, ƙasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka haɗa da haɗin gwiwa kan horar da sojoji da tsara manufofin ƙasashen waje da manyan makarantu da sai sauransu.

Turkiya da Najeriya mai yawan jama’a a nahiyar Afirka  na da kyakkawar alaka diflomasiyya tun daga ranar 9 ga watan Nuwamba shekarar 1960.

Ko a baya-bayanan Najeriya ta ƙarfafa alakar tsaro da Turkiya, inda rudunar Sojan Sama ta Najeriya ta sayi jiragen sama marasa matuƙa da jiragen yaki masu saukar angula guda shida daga Türkiye.

Ana ɓangaren Turkiyya, kamfanonin ƙasar sun daɗe suna aiki a fannin gine-gine da makamashi da tufafi, da masana’antu a Najeriya, suna fitar da kayayyaki kamar ƙarafu da injina da abinci, yayin da suke shigo da ɗanyen mai da kayan noma.

Wani batu da ya ɗauki hankali yayin wannan ziyara, shine, ɗan tuntube da shugaba Tinubu ya yi har ya taɓa ƙasa, wanda bai hana shi ci gaba da gudanar da abin da ya kai shi ba, sai dai ƴan Najeriya sun ci gaba da tafka muhara a kafofin sada zumunta dangane da koshin lafiyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com