Dakarun tsaro a Nijeriya da suka hada da ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro na cigaba da samun nasara kan tabbatar da ingantaccen tsaro a yankuna 6 na Nijeriya.
Wannan na cikin wata takardar jawabin tsaro darakta yada labaran rundunar sojin Nijeriya Manjo Janar Benard Onyeuko ya sanyawa hannu mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Yunin 2022, wadda taya tana kunshe da jawabin tsaron tun daga 19 ga watan mayu zuwa 2 ga yunin shekarar.
Takardar sanarwar tace dakarun Operation Hadin kai a ranar 22 ga wata mayun wannan shekara tare da hadin gwuiwar Civilian task force sun fatattaki ‘yan ta’adda a maboyar su dake garuruwan Amdaga, balazola, Ndakaine, jango, Sabah da Gobara duk a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda yan ta’addar suk aranta a na kare tare da barin kayayyakin su.
Read Also:
Har ila yau, a ranar 23 ga watan Mayu, 2022, sojoji sun gudanar da sintiri a kan titin tsohowar Marte dake karamar hukuma marte a jihar borno inda suk sami nasara kwato wata mota mallakin hukumar lura da tituna ta jihar da ‘yan ta’adda suka sace a watan fabrerun 2021.
Haka zalika sojojin dake sintiri a yankunan Ashigashiya, kodele, da apagaluwa dake cikin karamar hukumar Gwoza sunyi ta jihar Borno sun yi arangama da ‘yan Ta’addan inda sukayi kazamin artabu har ‘yan ta’addan suka ranat a na kare, yayin da sojojin suka sami nasarar kwato raguna 40.
Cikin wasu makwanni sojojin suka sake gudanar da wani sumame gami da kwanton bauna a yankin Zuyel-Wuno daura da tsaunin shelmi a kauyen Dugushewu, Gwoza, limankare a tsohowar Marte, Sabah, Kancorner, hanyar Gamboru Wulgo, Charaman, hanyar Pulka-Kwadaje, mairammi Tumbun rago, Tumbum Dilla da Jamina, Kawuri Sibiri, Kuwaitu, Kauyen Miya duk a jihar ta Borno.
Daga bisani Oyeuko ya yaba da da kokarin dakarun sojin kasar, tare da tabbatar da sake basu cikakkiyar gudunmawa, tare da godewa daukacin Al’ummar kasar bisa gudunmawar da suke bawa dakarun sojin a kokarin da suke na samar da ingantaccen zaman lafiya mai dorewa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 43 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 24 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com