CISA ta yaba da matakin da Sojoji suka dauka kan barayin man fetur A Nijeriya

Wata kungiyar mai zaman kanta mai lakabin Citizen’s Initiative for Security Awareness (CISA) ta yaba da tsauraran matakan da sojojin Nijeriya ke dauka na dakile barnar da masu fasa bututun mai, da kuma masu fashin teku da sauran masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Haka kuma kungiyar ta kalubalanci kiran da wasu kungiyoyi suka yi na sallamar babban hafsan hafsoshin Nijeriya Janar Lucky irabo kan kone jirgin da aka kama da laifin satar mai a yankin Neja Delta.

PRNigeria ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne, rundunar sojin kasar ta bayar da Umarnin lalata wani jirgin Ruwan dakon mai da aka kama da laifin satar mai a wasu boyayyun wurare a yankin Nijer Delta.

Kamen jirgin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cigaba da fahimtar yadda ake gano bututun mai da aka samar ba bisa ka’ida ba, wanda ake satar danyen mai da su wanda akwo yanzu ba’a bayyana wadanda ke da alhakin samar da bututun ba.

ba tare da bata lokaci ba sojoji sun kona jirgin ruwa da aka kama da laifin cin amanar kasa domin aika sakon gargadi ga masu ta’adar cin dinduniyar tattalin arzikin Nijeriya.

A cewar CDS, an kama kayan aikin tare da lalata su a matsayin wata hanya ta nuna yunkurin da sojoji suka yin a magance munanan laifuka da satar mai.

Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannu kodinetan kungiyar na kasa, Chidi Omeje da sakataren ta, Olasunkanmi Ogunbodede mai take “suka ga kokarin dakarun sojojin domin dakile kokarin da suke na yaki da masu yiwa tattalin Arzikin kasa ta’annati CISA tayi Allah wadai da kakkausar murya kan kokarin da wasu mutane ke yi ta hanyar amfani da rahoton kona jirgin ruwa da aka kama da laifin satar mai a matsayin wukar kugu don yin gangami.

Kungiyar ta bayyana cewa, wadannan mutane kuma suna kokarin yin katsalan kan ayyukan babban hafsan Tsaron kasar, Janar Lucky Irabor, wanda suke kira da a tsige shi  saboda yunkurin sa na daukar matakan da suka dace.

PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 56 minutes 35 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 38 minutes 0 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com