Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayar da tallafin dala 150,000, kwatankwacin naira miliyan 75 don yaƙi da yaɗuwar cutar mashaƙo a Najeriya.
Haka kuma gami taimaka wa al’umomin da suka kamu a jihohin Kano da Katsina da Legas da kuma Osun.
Tarayyar Turan ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwar yaɗuwar cutar a Najeriya tun farkon shekarar 2023.
Read Also:
Za a bayar da tallafin ne ga mutane sama da miliyan daya da rabi, inda za a fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Waɗanda ke zaune a wurare masu wahalar zuwa, kamar yadda ƙungiyar ta EU ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Tallafin wani ɓangare ne taimakon da ƙungiyar ke haɗawa na tara asusu don magance aukuwar bala’o’i a ƙasashen duniya ta hanyar ƙungiyoyin Red Cross da Red Crescent.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 35 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 17 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com