Kada ku shiga cikin ‘yan fashi da makami da sunan zanga -zanga – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya bayyana cewa baza su bari a gudnar da zanga –zanga da ake shirin farawa daya ga watan agusta a birnin ba, saboda ranar 1 ga watan Agusta rana ce ta karrama sarakunan gargajiya a birnin.

Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai bayan kamala taron tsaron birnin, wanda ya sami halartar karamar ministan birnin. Dr. Mariya Bunkure, jamián hukumar dake lura da birnin ta FCTA, shuwagabannin kananan hukumomi da sauran jamián tsaro a birnin.

Ministan ya bayyana cewa a wannan rana suna sa ran ziyartar aikin hanyar Saburi dake kusa da Dei-Dei a cikin kwaryar birnin na Abuja wato Abuja Municipal Area Council (AMAC), in da ya bukaci mazauna yankin kada su shiga cikin ýan fashi da makami don gudanar da zanga zanga.

“ka da ku bi wadannan ýan fashin da makami kan hanya, wadanda ke ikirarin gudanar da zanga –zanga. Babu wani abu zanga zanga. Abuja baza ta zama guda cikin yankunan da za’a gudanar da ita ba. Abinda kuke bukata shine shugabanci na gari, kuma muna yi muku abinda kuke bukata,’’

PRNigeria Hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 48 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 29 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com