Mahukunta a ƙasar Comoros sun ce shugaba Azali Assoumani ya fita daga cikin yanayi na haɗari bayan da wani matashi, ɗan sanda mai shekaru 24 ya daɓa masa wuka.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Harin ya auku ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 11 na safe agogon GMT a garin Salimani Itsandra, da ke arewacin babban birnin ƙasar, Moroni, inda ya ke halartar jana’izar wani shehin malamin addinin Islama.
A wani taron manema labarai, ministan makamashi na ƙasar, Aboubacar Said Anli ya ce shugaban ba ya cikin wani ƙalubale na rashin lafiya bayan ɗinki da aka masa a inda wuƙar ta same shi.
Sai dai rahotanni sun ce an samu matashin da ya kai wa shugaba Asoumani hari a mace a inda ake tsare da shi.
PRNigeria Hausa










