Wata kotu a Abuja ta soke tare da sakin yaran nan guda 26 tare sauran mutanen da gwamnatin ƙasar ta tuhuma da cin amanar ƙasa a ranar Juma’a.
Ana tuhumar mutanen ne 72 sakamakon zargin su da laifin ɗaga tutar Rasha a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa ta #Endbadgovernace a Agusta. Waɗanda ake tuhumar dai sun musanta aika laifin.
Sakin ya biyo bayan umarnin da shugaba Tinubu ya bayar ranar Litinin cewa a sake su sannan kuma a miƙa su ga ma’aikatar jinƙan ƙasar domin kula da walwalarsu sannan ta sada su da mahaifansu tare da binciken dalilin da ya sa aka tsare su na tsawon lokaci alhali yara ne.
Tuni dai an miƙa yaran 26 tare da sauran manya fiye 50 ga ma’aikatar jinƙai.
Tunda farko dai ministan shari’ar Najeriya ya saka baki a batun inda ya nemi a mayar da kyas ɗin ofishinsa domin tabbatar da sakin yaran.
Wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun shaida cewa yaran sun kasance a tsare a hannun ƴansanda tun watan Agusta, wani abu da ke janyo kiraye-kirayen a nema musu haƙƙinsu.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran nan da gwamnatin Najeriya ta tuhuma da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa ta ce ta yi farin ciki da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya ce a sake su.
Kafin ta je Abuja, Fatima ta ce an kira ta an faɗa mata ɗaya daga cikin ‘ya’yan nata ba shi da lafiya. Bayan ta isa kuma, kullum sai ta je wurin da ake tsare da su.
“Tun da na zo Abuja ban koma gida ba, kullum sai na je wajensu. Wani lokacin ma sai na je na yi bara kafin na samu abin da zan kai musu.
“Lokacin da na fara zuwa, da kyar aka bari na ga ɗaya daga cikin yaran nan kuma sai da na ba da kuɗi. Wani lokacin N1,000 ma ba ta isa, korar mu suke yi har sai ka samu masu kirki ne za su ƙyale ka,” kamar yadda ta yi bayani.
Ta ce tun yaran suna ƙanana aurenta da mahaifinsu ya mutu, kuma yana can kwance yana jinya sakamakon cutar shanyewar ɓarin jiki.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce kama yaran ya saɓa wa dokokin ‘yancin ɗan’adam na ƙasa da ƙasa, kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sake “nan take ba tare da wani sharaɗi ba”.
Malam Isa Sanusi, shugaban kungiyar a Najeriya, ya bayyana wa BBC cewar sun kuma nemi a biya diyya saboda “gallazawa da galabaitarwa da yaran suka fuskanta tsawon lokacin da ake tsare a cikin watan Agustan”.
Kwana ɗaya bayan sukar da gwamnatin ta sha, Antoni janar kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Lateef Fagbemi, ya nemi rundunar ‘yansandan ta miƙa masa lamarin domin cigaba da bibiyar shari’ar.
A ƙarshen mako kuma sai ga Ministar Mata Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ziyarci yaran, inda aka gan ta a hotuna tana raba musu ruwa da abinci tare da cin alwashin yi musu adalci.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 10 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 51 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com