Hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Lucky Aiyedatiwa na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammcin Najeriya.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa mista Aiyedatiwa – wanda shi ne gwamnan jihar mai ci – ya cinye duka ƙananan hukumomin jihar 18.
Babban jami’in tattara sakamakon, Farfesa Olayemi Akinwunmi, shugaban jami’an gwamnatin tarayya da ke Lokoja, ya ce Aiyedatiwa ya smu ƙuri’a 366,781, yayin da Agboola Ajayi na PDP ya samu ƙuri’a 117, 845, sai jam’iyyar LP da ta samu ƙuri’a 1,162.
”Bayan samu ƙuri’u mafiya rinjaye a zaɓen tare da cika duka sharuɗan da hukumar zaɓe ta ginda, a nan nake ayyana Lucky Aiyedatiwa na APC a matsayin wanda ya lashe wannan zaɓe”, in ji Farfesa Akinwunmi.
Read Also:
an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma babu labarin wani tashin hankali a sassan jihar a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.
A ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne hukumar zaɓen Najeriya ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ce mutum miliyan 2,053,061 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, yayin da matasa ke da kashi 35.41 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar zaɓen.
Jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya na da ƙananan hukumomi 18.
Jam’iyyu 18 ne suka fafata a zaɓen na yau, sai dai ana ganin fafatawar ta fi zafi tsakanin ‘yan takara biyu, wato gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa na APC da Agboola Ajayi na PDP.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1249 days 4 hours 6 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1231 days 5 hours 48 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com