Sanata Buba Ya Yi Kira da Zaman Lafiya Bayan Kama Masu Bata Masa Suna

Sanata Shehu Buba ya yaba wa jami’an tsaro bisa kama mutanen da suka shirya wani kamfen na batanci damanufar bata masa suna da kuma wasu mutane.

Sanata Buba, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaro da Leken Asiri, ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu zaman lafiya, su dinga tabbatar da sahihancin bayani kafin yada shi, tare da mai da hankali kan matsalolin da ke damun al’umma.

“Na dade ina tsayawa kan zaman lafiya da jin daɗin al’ummarmu. Ina ƙaryata waɗannan zarge-zarge marasa tushe, kuma zan ci gaba da aiki don ci gaban Bauchi ta Kudu,” in ji shi.

Jami’an tsaro kwanan nan sun kama wasu masu tasiri a kafafen sada zumunta da ake zargin suna da hannu a kamfen ɗin bata suna da ake kai wa wasu ‘yan siyasa, ciki har da Sanata Buba.

An yi wannan kame ne bayan bincike mai zurfi da ya haɗa da bibiyar sakonnin kafafen sada zumunta da kuma asusun da ake dangantawa da yada bayanai na ƙarya da kalaman kiyayya.

Sanata Buba musamman an zarge shi da alaƙa da ‘yan bindiga. Duk da ya sha musantawa, waɗanda suka bata masa sunan suna ci gaba da yada ƙarya a kafafe daban-daban kafin hukumomi su shiga tsakani.

Masu laifin sun yi amfani da bidiyon da aka shirya da gangan don yada labaran ƙarya domin ɓata masa suna a cikin majalisa da kuma wajen shirye-shiryen zaben 2027.

Bayan an kama su a wasu jihohin Arewa, wasu daga cikin masu yada bayanan sun amsa cewa an yaudare su ta hannun mutanen da suka yarda da su. Waɗanda aka ba beli sun riga sun fito da bidiyo da rubuce-rubucen neman afuwa a shafukansu na kafafen sada zumunta.

A cikin wani bidiyo, ɗaya daga cikinsu mai suna Nasiru Ontop ya ce:

“Mun yi kuskure mai girma wajen yarda da Kibanna, wanda ba mu san shi sosai ba. Bayanansa duk na jabu ne. Sai bayan an kama mu muka fara shakkar gaskiyarsa.

An goge asusun TikTok ɗinsa yanzu. Mun aikata abin da bai dace ba bisa bayanan ƙarya da bayanansa na jabu, saboda haka muna neman afuwa ga Sanata Shehu Umar Buba da duk wanda abin ya shafa,” in ji shi.

Abdulrashid Abdullahi Kano, wanda ke anfani da shafin Facebook mai suna Vanguard Hausa, shima ya fitar da sanarwa yana cewa:

“Mun tabbatar cewa bidiyon da ke zargin Sanata Shehu Buba Umar ƙarya ne kuma na bata suna ne.

An ƙirƙire shi ne daga maƙiyan zaman lafiya domin su ɓata masa suna. Sanata Buba ya kasance mai himma wajen inganta zaman lafiya da sulhu, yana aiki tare da malamai da shugabannin al’umma wajen warware rikice-rikice a Bauchi ta Kudu.”

Zagazola Makama

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com