ADC ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji

Jam’iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC ta nuna damuwa kan abin da ta kira gazawa iri-iri da ’yan Najeriya ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji nan take.

Jam’iyyar ta ce aiwatar da sabuwar dokar haraji zai ƙara tsananta matsin rayuwa ne kawai ga talakawa ba.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta jaddada buƙatar tattaunawa a faɗin ƙasa da ƙungiyoyin ƙwadago da na fararen hula da ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa da ƙwararru, da kuma gwamnatocin jihohi.

Jam’iyyar ta ce “Dole ne a saurari ra’ayoyin waɗannan ɓangarori kafin ɗaukar duk wani mataki kan aiwatar da sabuwar dokar harajin.”

“Jam’iyyar ta kuma buƙaci bayyanannun matakan kariya da za a ɗaure kai tsaye ga duk wani sabuwar dokar haraji, domin kare talakawa daga ƙarin nauyin rayuwa.” in ji sanarwar.

ADC ta ce “Duk wani sauyi a tsarin haraji ya kamata ya rage wahala ne ba ƙara jefa jama’a cikin talauci ba.”

Haka kuma, ADC ta buƙaci gwamnati ta mayar da hankali kan harajin kayan alatu da ribar da ta wuce kima da kamfanonin da ke da rinjaye, da yaƙi da cin hanci da rashawa maimakon ɗora haraji kan talakawan da ke fama da tsadar rayuwa.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa dole ne a samar da ƙaƙƙarfan kariyar doka domin kare haƙƙin masu biyan haraji.

Ta kuma yi gargaɗin cewa idan aka tilasta aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin ba tare da dakatarwa da tattaunawa ba, gwamnati ce za ta ɗauki alhakin duk wani abu da ya biyu baya na zamantakewa da tattalin arziki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com