Home Taska ‘Yan Daba Sun Farmaki Kasuwar Sayar da Wayoyin Hannu a Jihar Kano

‘Yan Daba Sun Farmaki Kasuwar Sayar da Wayoyin Hannu a Jihar Kano

Farm Center

‘Yan Daba Sun Farmaki Kasuwar Sayar da Wayoyin Hannu a Jihar Kano

 

Kano, Nigeria – Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari fitacciyar kasuwar sayar da wayoyin hannu watau Farm Center da ke cikin kwaryar birnin jihar Kano.

Rahotanni da ba a tabbatar da su ba, sun nuna cewa wasu daga cikin maharan sun fito ne daga wani taron siyasa da aka gudanar , sai dai babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.

Matakin da jami’an tsaro suka dauka

Daga bisani, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin, inda suka tarwatsa maharan tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar ta Farm Center.

Wata majiya a kasuwar ta shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa, ana zargin ƴan daban sun halarci wani taron siyasa da aka yi a yankin, kafin su farmaki wajen siyar da wayar da ke Yoyo Plaza.

Majiyar ta kara da cewa, ƴan daban sun daka wawa tare da kai sara ga ƴan kasuwar dake tsaka da ciniki, haka kuma, sun dinga kwacewa mutane wayoyinsu a kan hanya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu tabbacin mutuwar kowa, amma an ce mutane da dama sun samu raunuka Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba tukuna, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
'Yan Daba Sun Farmaki Kasuwar Sayar da Wayoyin Hannu a Jihar KanoFarfesoshi Adamu da Pate: Manyan Gwarzayen Ilimin Sadarwa Masu Taimako Daga Yushau A. ShuaibKotu: Shuaib ya ƙi Buƙatar NIPSS na Shirin Kwace Makullin Ɗakinsa a Shari’ar SEC 47Binciken Gaskiya: Shin Faɗan Oba Femi da Brock Lesnar a Wrestlemania Gaskiya ne ?An Ceto Marayu 15 Daga Hannun ƴan Bindiga a Jihar Kogi'Yan Bindiga sun Kashe Fasto da Iyalansa a Jihar PlateauCikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a NajeriyaIdan Suna Buƙatar Tattaunawa, sa kira mu - Trump ga Iran'Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai a Jami'ar OOUAn Kama Mai Taimakawa 'Yan Kungiyar Lakurawa Wajen Samun Kudi a Jihar Sokoto2027: Jam’iyyun Adawa Sun Sanar da Shirinsu na Yakar Tinubu da APC'Yan Siyasa ba sa yi wa Talakawan da Suke Jagoranta Adalci - Sanata NingiRahoton ‘Yan Sanda ya Danganta Kashi 70% na Laifuka a Kano da Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi, Ya Gano Mutane 513 da ake Zargin Masu Safara NePantami Ya Samu Karfin Gwiwa Yayin Da Jama'a Ke Taya Shi Murna a Lokacin Ziyarar Ayyuka a GombeMa’aikatar Tsaro ta yi Karin Bayani Kan Yarjejeniyar Yaki da Ta’addanci da Turkiyya, ta Karyata Zargin ‘Jihadi’
X whatsapp