Matsalar Tsaro: An Kashe Manoma 6 a Jihar Kaduna
Harin ya sake jefa al’ummomin yankin cikin jimami da fargaba, duk da ƙoƙarin da ake yi na dawo da zaman lafiya.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe manoma shida yayin da suke aiki a gonakinsu a yankin Kujijiro da ke Gundumar Kuyello ta Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Ƙungiyar Birnin Gwari Emirate Progressives Union (BEPU) ta tabbatar da harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da tayar da hankali.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Dakta Isa Muhammad, ya fitar, ya ce harin ya sake jefa al’ummomin yankin cikin jimami da fargaba, duk da ƙoƙarin da ake yi na dawo da zaman lafiya.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-hare kan manoma na iya hana mutane komawa gonakinsu a wannan kakar noma, lamarin da ka iya shafar samar da abinci da kuma ƙara tsadar rayuwa.
BEPU ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna da su ƙara kaimi wajen magance matsalar tsaro a Birnin Gwari da maƙwabtanta.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.











