Home Taska Manyan Tsofaffin Jami’an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan...

Manyan Tsofaffin Jami’an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan Ta’adda

'Yan Ta'adda

Manyan Tsofaffin Jami’an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan Ta’adda

 

Najeriya – Garkuwa da mutane da shiga kauyukada ƴan bindiga da sauran ƴan ta’adda ke yi ya jima da tsallake kan fararen hula, zuwa kan sojoji, ƴan sanda da sauran tsofaffin jami’an tsaro.

Rahoton This day ya nuna cewa manyan jami’an tsaro da dama da suka ajiye aiki sun fada komar ƴan bindiga, har ta kai ga rasa rayukan wasu daga cikinsu.

Wasu daga cikin jami’an da aka sace sun rasu, wasu kuma an karbe su nan take, yayin da waɗansu suka shaki iskar ƴanci, amma akwai wanda har yanzu ke tsare a hannun ƴan bindiga.

Manyan jami’an da suka shiga hannun ƴan bindiga

1.Manjo Janar Idris Alkali

Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya) ya yi aiki a matsayin Shugaban Gudanarwa a Hedikwatar Sojoji da ke Abuja a lokacin aikinsa na soja.

Jaridar Punch ta wallafa cewa ya ɓace a ranar 3 ga Satumba, 2018, sannan daga bisani aka gano gawarsa a ranar 31 ga Oktoba, 2018 a wat rijiya da ɓata-gari suka jefa ta.

Janar Alkali, wanda ke kan hanyar tafiya daga Abuja zuwa gonarsa a Jihar Bauchi da motarsa Toyota Corolla, ya bi ta yankin a Jos, inda ake sa ran cewa a nan ne aka kama shi, aka kashe shi tare da jefar da gawarsa.

Bayan bincike mai zurfi da Sojojin Najeriya suka gudanar, an gano gawarsa a cikin wani rijiyar da aka watsar a Guchwet, Shen, a Jos ta Kudu, a ranar 31 ga Oktoba, 2018.

An yi jana’izarsa a makabartar Gudu da ke Abuja a ranar 3 ga Nuwamba, 2018, kamar yadda addinin Musulunci.

2. Air Chief Marshal Alex Badeh

Premium Times ta wallafa cewa tsohon Shugaban Hafsan Tsaron Ƙasa, Air Cif Marshal Alex Badeh (mai ritaya), ya gamu da miyagun mutane, inda aka kashe shi a ranar 18 ga Disamba, 2018, a kan hanyar Abuja–Keffi yayin da yake dawowa daga gonarsa.

3. Air Vice Marshal Muhammad Maisaka

Rahoton Daily Post ya bayyana cewa ƴan bindiga sun hallaka tsohon Air Vice Marshal Muhammad Maisaka tare da jikansa a Rigasa, Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, a ranar 8 ga Nuwamba, 2021.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon jami’in yana murmurewa daga wata rashin lafiya da ta sa ya shafe fiye da shekaru uku yana fama da shanyewar jiki.

Maisaka, wanda ya taɓa zama Daraktan Horarwa da Ayyuka na Likitanci a Hedikwatar Tsaro, an kashe shi ne a wani hari da ya girgiza rundunar soja.

4.Kanal Rabi’u Garba Yandoto

TVC News ta ruwaito cewa a ranar 1 ga Janairu, 2023, wasu ’yan bindiga sun sace tsohon jami’in soja Colonel Rabi’u Garba Yandoto tare da ’ya’yansa biyu a kan hanyar Gusau–Tsafe a Jihar Zamfara.

Da farko masu garkuwa sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 50, amma daga baya suka sauko. A ranar 10 ga Janairu, 2023, Kanal Yandoto da ’ya’yansa sun shaki iskar ’yanci bayan an biya fansa da aka ce ya kai kusan Naira miliyan 10.

5. Manjo Janar Richard Duru

Kafar Channels TV ta wallafa cewa an sace tsohon Manjo Janar Richard C. Duru a Owerri, Jihar Imo, a watan Satumba 2023.

An sace shi ne a Bishops’ Court, Area 7, Orji/Uratta, Owerri, yayin da aka kuma sace motarsa kirar Mercedes-Benz GL 450 mai lamba LND 826 NG.

Duk da rahotannin cewa an biya kuɗin fansa na dala 50,000, daga bisani masu garkuwar suka kashe shi. Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta ce an kama waɗanda ake zargi bayan an yi aiki tare da sashen yaki da garkuwa da mutane.

6. Birgediya Janar Uwem Udokwere

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa an kashe Brigediya Janar Uwem Harold Udokwere (mai ritaya) a ranar 22 ga Yuni, 2024, lokacin da ’yan fashi suka kai hari gidansa da ke Sunshine Homes Estate a yankin Lokogoma, Abuja.

Mafarautan sun caka masa wuƙa har ya rasu yayin da yake ƙoƙarin kare iyalinsa, sannan suka tafi da bindigarsa da wasu kayayyaki masu daraja.

A ranar 24 ga Yuni, 2024, rundunar ’yan sandan FCT ta gabatar da mutane huɗu da ake zargi—Ibrahim Rabiu, Nafiu Jamil, Aliyu Abdullahi, da Mohammed Nuhu.

7.Birgediya Janar Maharazu Tsiga

Garkuwar tsohon Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), a watan Fabrairu 2025 ta ja hankalin ƙasa kusan baki ɗaya.

An sace Tsiga a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, a garinsu Tsiga da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, tare da wasu mutum tara.

Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, rahotanni sun bambanta kan ainihin adadin da aka nema da wanda aka biya.

Daga bisani ya samu ’yanci a ranar 3 ga Afrilu, 2025, bayan shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa.

8. Manjo Joe Ajayi

Jaridar Vanguard ta ruwaito an sace Manjo Joe Ajayi mai shekaru 76 daga gidansa da ke Odo-Ape, Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu a Jihar Kogi a ranar 21 ga Mayu, 2025.

Hukumar ’yan sandan jihar Kogi ta tabbatar cewa ya rasu a hannun masu garkuwa duk da cewa iyalansa sun biya Naira miliyan 10 a matsayin fansa. An gano gawarsa sannan aka ajiye ta a asibitin Kabba kafin aka yi masa jana’iza.

9. Kanal Joseph Ajanaku

A watan Janairu 2026 ne aka sace tsohon Colonel Joseph Ajanaku daga gidansa da ke gaban cocin Salvation Army a kan titin Rukuba a Jihar Filato, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

Masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200 tare da barazanar kashe shi idan sojoji suka ci gaba da aikin ceto ta hanyar karfi.

Daga bisani jami’an tsaro sun canza salo zuwa aikin sirri kuma suka kuɓutar da shi a kusa da Rafiki a Ƙaramar Hukumar Bassa da misalin 5:30 na yamma a wannan rana.

10.Manjo Janar Rabe Abubakar

BBC ta wallafa cewa an sace Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), tsohon Daraktan Yada Labaran Tsaro kuma tsohon kakakin Rundunar Sojin Najeriya.

Jami’in soja mai ritaya tare da matarsa suna tafiya a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu a ranar 30 ga Mayu, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai musu kwanton ɓauna.

Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun tare motarsu sannan suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Hukumar ’yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an bude wuta yayin harin, lamarin da ya tilasta direban ya tsere.

Rahotannin da ke shigowa yanzu sun bayyana cewa Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun masu garkuwa da shi, kamar yadda gwamantin jihar Katsina ta tabbatar.

A zantawa da Legit, Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida ya bayyana cewa ana wasu shirye shirye a halin yanzu, saboda haka ba zai iya bayar da cikakken bayani game da lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Manyan Tsofaffin Jami'an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan Ta'addaTarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun ƴan BindigaMatsalar Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Babbar Hanyar AbujaDuk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da 'Yan Ta'adda, za a ɗauke shi a Matsayin ɗan ta’adda - Christopher MusaFarashin ɗanyen Mai ya Faɗi Bayan Amurka ta Soke Sabbin Hare-Haren kaiwa IranAmurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran - TrumpMajalisar Wakilan Najeriya ta Amince da ƙudirin Dokar Kafa ’Yan sandan JihaHukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar NejaMiyagun ƙwayoyi da Makamai: Jami'an Tsaro Sun Kama Mutane 8 a Jihar YobeAbin da Obi ya Fada Kan Atiku - Dele MomoduHukumar EFCC ta Gurfanar da Ma'aurata Kan Damfarar Kudi Kusan N2bnFiye da Kashi 60 na 'Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara - IMFGwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasartaƳan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a ZamfaraMayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a Sokoto
X whatsapp