Home Taska Ta’addanci: Za a Gurfanar da Mutane 400 a Gaban Kotun Tarayya da...

Ta’addanci: Za a Gurfanar da Mutane 400 a Gaban Kotun Tarayya da ke Abuja

Court

Ta’addanci: Za a Gurfanar da Mutane 400 a Gaban Kotun Tarayya da ke Abuja

 

Aƙalla mutum 400 ne za a gurfanar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan kan zargin aikata laifukan ta’addanci, a ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta’addanci da aka taɓa yi a Najeriya.

Shari’ar na nuni da wani muhimmin mataki a ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma magance matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita tsawon lokaci.

Waɗanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da kai hare-hare da tallafawa ayyukan ƙugiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ta’addaci.

Wannan na zuwa ne bayan wata babbar shari’a a watan Afrilun 2026, inda aka gurfanar da sama da mutane 500 kan zargin aikata laifukan ta’addanci kuma an samu kusan 400 da laifi.

Mahukunta sun ce wannan mataki na da nufin kammala sauran shari’o’i da kuma gurfanar da ƙarin waɗanda ake zargi domin a hukunta su.

Najeriya na ci gaba da fama da rikicin ta’addanci na tsawon shekaru 16, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu, yayin da matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp