Home Taska Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP – Rundunar Sojin Najeriya

Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP – Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar Soji

Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP – Rundunar Sojin Najeriya

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas ta ceto mutum 47, yawancinsu mata da ƙananan yara, da mayaƙan ISWAP suka tsare a yankin Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen ne a ranar 20 ga watan Yuni 2026, bayan wani gagarumin samame da sojojinta suka kai wanda ya tilasta ‘yan ta’addar tserewa suka bar waɗanda suka sace.

Ya ce hare-haren kasa da na sama da dakarun suka kai wa sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi ne ya sa ‘yan ta’addar suka rikice suka bar wuraren da suke, lamarin da ya bai wa wadanda aka tsare damar tsira bayan dogon lokaci a hannunsu.

A yanzu haka, an kai waɗanda aka ceto wuraren tsaro inda ake basu kulawar lafiya da taimakon jin kai, yayin da rundunar ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP - Rundunar Sojin NajeriyaSanatocin za su Fara Duba ƙudirin  Kafa ƴan Sandan Jihohi Ranar Laraba - AkpabioMatakin da Amurka ta ɗauka na Cire Tallafin Cutar HIV a Afirka ta Kudu Zai Janyo Asarar Rayuka - MDDAn Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban JosMatsalar Tsaro:  An Kashe Manoma 6 a Jihar Kaduna An Zargi Kwankwaso da Sayen Fom ɗin Takara na Kujeru 69 a Jam'iyyar PRPƘasurgumin ɗan bindiga, Turji ya ɗauki Alhakin Kashe Sojoji a Jihar SokotoMasu Iƙirarin Jihadi Sun Hallaka Manoma 11 a Jihar Borno 'Yan Bindiga sun ƙone shingen Jami'an NSCDC Tare da Garkuwa da Mutum 1 a Jihar KebbiTaron NUJ: Lokacin Da Manyan Jami’an Tsaro Suka Guji Yan Jarida Daga Yushau A. ShuaibSamar da Tsaro: Sojojin Najeriya sun Kama ƴan ƙasashen Wajen 46Ta'addanci: Za a Gurfanar da Mutane 400 a Gaban Kotun Tarayya da ke AbujaAn Ceto Matar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun ƴan BindigaHauhawar Farashin Kayan Masarufi a Najeriya ya ƙaru Zuwa Kashi 15.93Rundunar Sojin Najeriya ta Gudanar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ƴan Bindiga a Jihar Katsina
X whatsapp