Ministan Sadarwa ya Halarci Taron ƙungiyar ɗalibai Kan Harkokin Tsaro
Mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM) ya halarci babban taron shekarar 2022 na ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa, “National Association of Nigerian Students (NANS) a cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa, Abuja.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai girma Shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), shi ne ya wakilci ministan tare da gabatar da takarda mai taken: “Emerging Technologies: A solution to National Security” wato “Rungumar Fasahar Zamani: Mafitar Warware Matsalolin Tsaron Ƙasa”. Lahadi, 20 ga watan Maris, 2022.











