Home Labarai Tsaro: Rundunar Sojin Najeriya sun gano Naira Miliyan 60 da za a...

Tsaro: Rundunar Sojin Najeriya sun gano Naira Miliyan 60 da za a kai wa ‘Yan Bindiga Kudin fansa

Rundunar Sojin Najeriya ta ce Dakarunta sun bankado Naira Miliyan 60 da ake kokarin kai wa ‘yan ta’adda kudin fansar karbo wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Haka kuma, dakarun sun yi nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su da suka hadar da mata da kananan yara.

Dakarun, wadanda suka hada da sojin sama da na kasa, sun kai ga cin karfin ‘yan bindigar. Inda suka bankado tare da kwato muggan makamai da bindiga kirar AK47, da albarusai da sauransu.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewar, cikin wadanda ake zargin zasu kai kudin fansar  akwai jami’in tsaro na farin kaya wato DSS.

Wani jami’in liken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa dakarun sojin saman bataliya ta 271 a Birnin Gwarri, da Dakarun FOB na  Gwaska, sun kubutar da dimbin mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin atisayen na hadin gwuiwa.

Jami’in ya ce: “An kwato zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 60, Man Fetur da kuma muggan makamai, a yayin gudanar da aikin.

“Sauran kayayyakin da sojojin suka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hadar da Motoci, Bindigu kirar AK-47 Alburusai iri-iri da kuma wayoyin hannun.

“Za kuma a mika batun jami’an tsaron da suka hada da na DSS da ake zargi da kai kudin fansar ga ma’aikatar tsaron Najeriya, domin gudanar da bincike.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp