Home Labarai LAFIYA: Gwamnatin Adamawa ta Sanar da Kawo Kashen Cutar Kwalara

LAFIYA: Gwamnatin Adamawa ta Sanar da Kawo Kashen Cutar Kwalara

Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da kawo karshen barkewar cutar kwalara data addabi jihar.

Wannan ya fito ne ta bakin Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Isa Abdullahi, yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Yola Babban Birnin Jihar, inda yace cutar ta Kwalara ta barke ne a watan Yulin 2021, inda wata na gaba mutum 1,959 ake zargin sun kamu da cutar.

Ya zuwa ranar Alhamis, an sanar da kawo karshen barkewar cutar, wacce ta kama akalla mutum dubu biyu tayi sanadiyyar mutuwar mutane 55 a fadin jihar.

“Tun da  bamu sami rahoton bullar cutar kwalara ba, bayan sanya idanu da mukayi na tsawon makwannin Gwamanti da Abokan huldar ta, muna farin cikin sanar da cewa yanzu hakan babu cutar kwalara a jihar Adamawa.

Sai dai kwamishinan yace bayyana kawo karshen cutar ta kwalara, ba wai wata dama bace da al’umma zasu yi amfani da ita ba wajen shakatawa tare da yin watsi da dokokin da masana kiwon lafiya suka gindaya kan cutar.

Kawai wannan wata kofa ce ga mahukunta domin sake zage dantse wajen inganta shirye-shiryen magance dukkan cututtukan dake yaduwa, wajen samar da rigakafin su.

Daga bisani ya mika godiyar su ga Hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma Asusu tallafawa kananan ya rana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da dukkan wadanda suka hada hannu da gwamnatin jihar tun daga watan Yuli har kawo yanzu da yawan masu kamuwa da cutar ya ragu matuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp