Home Labarai TSARO: Dakarun MNJTF Sun Tarwatsa Maboyar Mayakan ISWAP

TSARO: Dakarun MNJTF Sun Tarwatsa Maboyar Mayakan ISWAP

Dakarun hadin gwuiwa na MNJTF sun yi Ruwan wuta kan sansanonin horas da mayakan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP  da matsugunnan kwamandojin su a yankin Tafkin Chadi.

Wata majiyar liken asiri ta shaidawa PRNigeria cewa, dakarun sojin kakarshin jagorancin Rundunar Sojin Saman Nijar sun kai harin ne a ranar Alhamis, 14 ga Afrilun, 2022, a Tumbun Rego.

“Wani bayanin sirri ya nuna cewa wurin da aka kai harin ya zama wurin da manyan kwamandojin ISWAP ke zama, harin daya kai ga kawar da  wasu cikin kwamandojin da suka hada da Ibn Usman, Hani Abdullahi, Ababak Shuwa, Abu Jibrilla da Abu Ali.

“tare da hadin Gwuiwa jiragen yaki na Rundunar Sojin Saman Nijar, Jiragen sun kai hari a kusa da wuraren dake zama mafakar mayaka da iyalan ‘Yan Ta’addan.”

“A ranar 15 ga watan Afrilu, 2022 Rundunar Sojojin Nijeriya karkashin Operation Lake Sanity suka gudanar da aikin kawar da ‘Yan ta’addan, inda tuni suka kwace iko da yankuna da dama da ‘Yan ta’addan suke mamaye a dajin Sambisa tare da cigaba da kai musu hare-hare a dajin Tumbun.

“Hare-haren jiragen sama da kuma ayyukan sojojin kasa sun I sanadiyyar mutuwan ‘yan ta’adda da dama inda wasu da dama suka sami muggan raunika

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp