Tsawon shekaru Uku bayan Ganduje ya amince da aikin da ware Naira Miliyan 381 na aikin Hanya mai tsaho kilomita daya ga kamfanin Stonegate, Kamfanin yace kawo yanzu ba’a bashi ko sisin kwabo a cikin kudin ba.
Daga: Usman Bello Balarabe Fassara: Rabiu Sani Hassan
Wani cigaba da aka samu kan rahoton wani zargi da Economic Confidencial ta wallafa a makon daya gabata, wanda ya bankado yadda Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da wadannan makudan kudade ga wani kamfani da bashi da rijista da Hukumar Yiwa Kamfanoni Rijista ta CAC, domin gyaran hanyar Ado Bayero dake Jihar Kano.
Binciken farko ya nuna cewa kimanin Naira Miliyan 110 aka amincewa kwangilar hanyar tsawon shekaru uku (2019,2020 da kuma shekarar 2021) kuma ana zargin an fitar da Naira Miliyan 38 a shekarar 2019. Wasu takardun da Economic Confidential ta samu sun tabbatar da hakan, wannan ya nuna cewa jumullar kudin kwangilar ya haura Naira Miliyan 381 a lokacin da aka fidda ita a shekarar 2018.
Duk da cewa a wancen lokacin jami’an Gwamnatin Ganduje sun gaza yin cikakken bayani kan kwangilar hanyar da aka ambata, sai dai kamfanin da aka ambata a cikin badakalar, wanda bincike ya bayyana baya cikin kundin rijistar hukumar ta CAC ya fito yayi takaitaccen bayani kan batun hanyar.
Manajan Kamfanin Engr. Yusuf Muhammad, ya bayyanawa jaridar Economic confidential cewa kamfanin nada rijista da hukumar ta CAC, kamfanin nada dukkan wasu takardu da ake bukata, sai dai kawai sun sauya sunan kamfanin ne daga Stonegate Quaries Ltd zuwa Stonegate Engineering and Quarries Ltd, abinda ya sanya a binciken da jaridar tayi kamfanin bai bayyana ba. A halin yanzu, tsohon suna da adireshin sune bayanan da dake dasu a jikin takardar kwangilar da allon dake Karin bayani akan ta.
Ta cikin wani rahoto da hukumar dake lura da yiwa kamfanonin rijista ta baiwa Economic Confidential tace kamfanin nada 1088975 tare da sunayen Walid khabbazi da Ibrahim Hazim matsayin darakta, sai John Erameh a matsayin sakatare.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sanya kamfanin bai fallasa badakar kwangilar ba, Dan kwangilar yace har yanzu ba su samu wani kudi daga Gwamnatin Jihar Kano ba, duk da cewa sun bi dukkan hanyar da ta dace wajen bindiddigin a biya su.
“Na gani a rahoton da kuka wallafa cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fidda kudin da suka kai Naira Miliyan 38 domin gudanar da aikin, amma kawo yanzu ba’a biyamu ko sisin kwabo ba, zaka iya zuwa ka bincika domin ka tabbatar.”
“Mun yi wannan bayani ne domin bama so wani batun siyasa ya sa sunan kamfanin mu ya baci, mun ajje kayan aikin mu a wajen aikin na tsawon shekara guda, mun cigaba da bibiya kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan batun, don haka muka nade hannayen mu muka zira idanu. Kamar yadda Engr Yusuf ya bayyana.
Read Also:
Ta cikin wata sanarwar takarda mai dauke da kwanan watan 4th ga watan Disambar, 2018 wadda Economic Confidential ta samu, ta bayyana yadda aka fidda kwangilar hanyar ta Ado Bayero dake Unguwar Dorayi Babba, cikin Karamar Hukumar Gwale, wadda ma’aikatar Ayyuka Gidaje da Sufuri ta samar, takardar ta bayyana sahalewar Majalisar Zartarwar Jihar Kano, wanda Gwamna Ganduje ya jagoranta wajen bayar da kwangilar ga kamfanin na StoneGate Quaries LTD (wanda yanzu ya koma StoneGate Engineering Quaries Ltd) akan Naira Miliyan 381, 904, 640.43 kacal domin kammala aikin a tsawon shekaru 3.
Haka zalika ta cikin wata takarda da Economic Confidential ta gani wadda ke dauke da sa hannu da tambarin biyan kudin Naira Miliyan 49 daga sashen Injiniyan ma’aikata na Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano zuwa kamfanin kwangilar na StoneGate Quaries Limited.
Kamar yadda bincike ya nuna cewa naira Miliyan 57,285,696 (Miliyan Hamsin da Bakwai da Dubu Dari Biyu da Tamanin da Biyar da Naira Dari Shida da Casa’in da Shida). Da ya kamata a biya na kwangilar na kashi 15 cikin 100 ya kamata a biya ga dankwangilar, amma takardar tace sai da dan kwangilar ya biya naira 7,638,092 (Miliyan Bakwai, da Dubu Dari Shida da Talatin da Takwas da Naira Casa’in da Biyu) a matsayin kudin shiga ga mai bada kwangila (Tender) ga dukkan alamu dai dan kwangilar bai biya kudin ba, domin an cire daga cikin kudin daga kashi 15 cikin dari na kudin nasa don haka adadin kudin, domin haka yawan kudin ya karu a takardar biyan kudin inda ya kai Naira Miliyan 49,647,000 (Miliyan Arba’in da Tara da Naira Dari Shida da Arba’in da Bakwai).
Ko a wannan karo dai kamar wancen lokaci Kwamishin Ayyuka na Jihar Kano Engr. Idris Wada Saleh yaki cewa komai, dukkan kokarin da mukayi domin ya amsa kira ko sakon karta kwana, yayi buris.
Idan dai za’a iya tunawa ta cikin rahoton da Economic Confidential, kwamishinan ta cikin martanin da yayi cikin fushi yacewa wakilin Mu “Kai waye ya gaya maka Dan Kwangilar bai cancanta ba? Shin aikin baya tafiya yadda ya kamata ne? ko kuma ce maka akayi dan kwangilar baya biyan haraji ne?”
Tambayoyin da ya kamata gwamnatinn Jihar Kano ta amsa, Tun da Dan Kwangilar da bakin sa yace bai karbi ko da sisin kwabo a cikin makudan kudin da gwamnatin ta ware ba, wannan ne ya sa suka bar hanya ba tare da sun yi wani aiki a kanta ba; to ina aka karkatar da kudin har Naira Miliyan 38 da aka fidar a shekarar 2019? Mene matsayin takardar biyan kudi ta naira Miliyan 49 wadda ke nuna cewa an biya Dan Kwangilar a matsayin kaso 15 cikin Dari na kudin Kwangilar? Ko wanne lokaci Gwamnatin jihar Kano ta yanke shawarar fasa sakin kudin ga dan kwangilar bayan an sami fitar takardar biyan kudin kwangilar? Ko dai wani batu ne da ake cewa wai bonono rufin kofa da barawo?
Ko mene makomar Al’ummar wannan yanki da hanyar take, kasancewar su ne ke cikin mawuyacin hali sakamakon lalacewar wannan hanya? Mene yasa aka sauya sunan Kamfanin Kwangilar? Ko yaushe ne za’a fara aikin titin mai tsawon kilomita daya da aka yi hasashen kammala shi cikin watanni Uku amma tsahon shekaru uku ba’a kammala shi ba?
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 15 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 56 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com