Home Labarai Gwamnatin Jihar Niger ta Tabbatar da Halaka ‘Yan Bindiga a Garin Shiroro

Gwamnatin Jihar Niger ta Tabbatar da Halaka ‘Yan Bindiga a Garin Shiroro

 

Wani rahoto ya bayyana cewa, hankalin Gwamnatin jihar Niger ya kai kan wani labari da ake yadawa a kafar sada zumunta ta zamani da sauran kafafen sadarwa, cewa wani harin Jami’an tsaro ta sama yayi sanadiyyar mutuwar wasu fararen hula a garin Kurebe dake Karamar Hukumar Shiroro a Jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da masarautu na jihar Emmanuel Umar, wadda aka aikewa PRNigeria.

Sanarwar tace Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a iyaka sanin ta babu wani farar hula daya rasa ransa sakamakon harin, haka kuma babu wani mazaunin garin da aka tilastawa shiga ko zuwa neman abinda zai ci a sansanin ‘ya gudun hijira a jihohi makotan jihar.

Gwamnatin Jihar ta Niger ta yi maraba da matakin kakkabe ‘Yan ta’adda da Rundunar Sojin Nijeriya ta dauka a  jihohin dake makotaka da jihar, da wasu kananan hukumomin jihar ciki harda kananan hukumomin Shiroro, Munya da sauran sun, matakin da yayi sanadiyyar kawar da ‘yan ta’adda masu tarin yawa a yankin.

Sanarwar tace gwamnatin jihar tayi matukar farin ciki da wannan  atisayen sakamakon nasarar da yake samu na halaka ‘yan bindiga a kananan hukumomin da lamarin ya shafa, wannan hadakar ta taimaka matuka wajen dakile ayyukan ‘yan ta’addan a kanana hukumomin Munya da Shiroro, tare da kubutar da wasu mutane da dama.

Daga bisani Gwamnatin Jihar ta nuna jindadin bisa nasarar da dakarun hadin Gwuiwar ke samu, tare da karin karfin gwuiwar cigaba da kakkabe su daga cikin Al’ummar dake yankin, domin su sami damar komawa gonakin su da cigaba da ayyukan su na yau da kullum.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp