Home Labarai Tsaro :Jirgin Sojin Sama ya Halaka Yara 6 a Jihar Niger

Tsaro :Jirgin Sojin Sama ya Halaka Yara 6 a Jihar Niger

Gwamnatin Jihar Niger ta tabbatar da mutuwar kananan yara 6 sakamakon wani hari da Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta kai bisa kuskure.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Matane ne ya bayyana mutuwar yaran, sakamakon harin jirgin saman. Inda yace lamarin ya auku ne makon daya gabata, inda bincike ya tabbatar da cewa yaran sun halaka ne sakamakon wani hari da dakarun sojin suka kai maboyar ‘yan Bindiga a jihar.

Lamarin dai ya faru ne a garin Kurebe dake karamar hukumar shiroro ta jihar Niger.

Ko da aka tambaye shi kan mutuwar yaran 6, cewa ko dai Dakarun Sojin Saman ne suka hallaka su: yace “ hakan zai iya kasancewa, don haka ne ma gwamnatin ke sake fadada bincike kan lamarin domin tabbatar da zahirin abinda ya faru.

A cewar shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin Karamar Hukumar ta Shiroro Salis Sambo, yayin da yake ganawa da manema labarai, yace Dakarun Sojin sun halaka yaran ne a kokarin da suke na tarwatsa ‘Yan Ta’adda wadanda suka gudu cikin al’umma domin tsira da rayuwar su.

Yace Kananan Yaran na kan hanyar su ta dawowa daga diban ruwa a wani gulmi, inda yace hudu cikin su ‘yan gida daya ne.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp