• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Labarai VIDEO: Yadda ‘Yan Ta’adda suka kori Mutum Dubu 10 Suka Halaka Mutum...
  • Labarai

VIDEO: Yadda ‘Yan Ta’adda suka kori Mutum Dubu 10 Suka Halaka Mutum Dari 2 a Jihar Kebbi

By
Prnigeria
-
May 3, 2022
Arewa Award

Wani bincike da jaridar PRNigeria ta gudanar ya bayyana cewa akalla mutane dubu 10 ne suka rasa mutsugunnan su  tsahon shekaru 3 da suka gabata, a jihar Kebbi dake Arewacin Nijeriya.

Kalli Video:

Mutanen sun rasa matsugunnin ne sakamakon wasu hare-hare da ‘Yan bindiga suka kaddamar a tsakanin kauyukan Chonoko da wasu yankuna a karamar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar.

Jaridar tace wani kisan kiyashi da ‘Yan bindigar suka fara kan Al’ummomin sun halaka mutum 200 tare da fatattakar kauyuka 42 a shekarar 2019.

Kauyukan sun hadar da Dan Kade, Warkata, Kurgiye, Ragam I, II da ta III, ‘Yar Kuka, Shangel, Tungan Dangula, Kahalmo I da ta II, Kadebo, Ched-Kubu, Yababa, Gimi, Ganyale I, II da ta III, Silabi da kuma  Digoga.

Sai kuma wasu kauyukan da suka hadar da; Bankunatare, Bawada, Zagami, Turame, Gyado, Tungan Kwando, Ketare, Sebzama I, II da ta III, Dhilo da kuma Duru.

Sauran sun hadar da; Tudun Wada, Digwengwe, Gaya, Saaki, ‘Yar Buga, Dilanko, Zuttu da Irgaa.

Wakilan jarida su biyu (2) da suka ziyarci garin na Chonoko, sun rawaito cewa tun daga lokacin ‘yan bindigar suka mamaye gidajen wadanda suka mutu ba tare da wani daukar mataki kan hakan ba.

A yayin da yake bayyanawa PRNigeria irin halin da ya shiga, wani tsoho mai kimanin shekaru 70 mai suna Mai Unguwa Maizuwa da aka kora daga kauyen Zagami ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shafe shekaru 3 a jere suna kai hare-hare a kan al’ummar tun daga shekarar 2019.

Yace “’yan bindigar bayan sun kore shanun su sun kuma yi awon gaba da dukiyoyinsu, baya ga hallaka mutane da dama, sannan kuma a ‘yan tsakanin nan sun kori kowa daga kauyen.

Mai zuwa yace “bayan haka yayi asarar wasu kayayyaki da suka hadar da buhunan siminti da dama da kuma wasu kudade da ya ajiye na kasuwanci, kimanin naira 997,000 a yayin harin

Read Also:

  • NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas
  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Mai zuwa dake da ‘ya’ya guda Shirin (20) yanzu haka yana rayuwa ne a sansanin ‘yan gudun hijra mai tarin cunkoso dake garin Chonoko.

Wani magidanci daya rasa Dan sa sakamakon wasu hare-haren ‘Yan bindiga a kauyen Kadebo, Musa Sarkin Makada, ya bayyana wa PRNigeria yadda suka shiga halin kakanakayi tun bayan da akayi awon gaba da Al’ummomin su.

An ruwaito cewa tun da aka kai hare-haren kauyen ya zama tamkar kufai, baya ga kwashe mata da kananan yara da tsoffi gami da nakasassu wadanda baza su iya guduwa ba domin tsira da rayuka su.

Shima da yake Magana a irin wannan yanayi na alhini, guda cikin shugaban al’ummar duk da ya nemi a sakaye sunan sa, ya bayyanawa PRNigeria cewa kawo yanzu ‘yan ta’addan na cigaba da cin karen su babu babbaka ba tare da an hukunta su ba; inda  suka kori wasu mutane da kauyukan su tare da kone  gidaje da kayayyakin abinci inda makarantu suka kasance a rufe.

“Baya ga hare-hare da garkuwa da mutanen kauyen, ‘yan bindigar na lalata gonaki da gidajen al’ummomin yankin da basu da karfi.

“Matsalar abinci da ake fuskanta babu shakka zata lakume rayukan mutane da dama, saboda an tilastawa dubban manoma hakura da gonakin su, kuma hakan ya rage ayyukan noman da ke matsayin hanya daya tilo ga mazauna yankin. Haka kuma an rufe makarantu a dukkan kayukan da al’amarin ya shafa, kaga wannan na taimakawa wajen kara yawan daliban da basu samin damar karatun.

“Bugu da kari, duk wannan ta’asa da ‘yan ta’addan ke aikatawa, babu wasu jami’an tsaro dake kokarin daukar mataki domin magance ayyukan su, yayin da hukumomin agaji da suka hadar da Red Cross da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA basu bayar da wani tallafi ga ‘Yan gudun hijirar musamman kayayyakin agaji da magunguna ga marasa lafiya da masu rauni.

“Yanzu haka dai mutanen da suka rasa matsugunansu basu da Muradin komawa gidajen sakamakon mummunan yanayin da suka fuskanta,” kamar yadda ya bayyana cikin tashin hankali.

A martanin da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA tayi kan wannan rahoto hukumar tayi alkawarin magance matsalolin da ‘yan gudun hijirar ke ciki da gaggawa, yayin da ICRC tace, sakamakon ayyukan jin kai da suke yi a yankin Arewa Maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya, kawo yanzu da basu sami damar mayar da hankali kan  Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba.

By PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • 'Yan Gudun Hijira
  • Chonoko
  • Kebbi
  • NEMA
  • Yan Ta'adda
  • Yara
Previous articleShugaban NITDA ya Halarci Bikin Sallah a Rana ta Biyu a Haɗejia
Next articleGidauniyar Malam Inuwa ta ba da Gudunmawar Mota ga Kungiyar Mata Masu Yaki da Cin Zarafin Mata da Kananan Yara
Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas

Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi

Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

Hukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru

NUPENG ta cimma matsaya da kamfanin Dangote

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya

El-Rufa’i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi

‘Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jihar

Kofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPP

Burkina Faso ta amince da dokar haramta neman maza a faɗin ƙasar

An bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan Satumba

Recent Posts

  • NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas
  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15
  • Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi
  • Hukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1551 days 14 hours 3 minutes 37 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1533 days 15 hours 45 minutes 2 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
NDLEA ta kama Ba'indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a LegasLikitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗiKotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin MauludiHukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar AnsaruNUPENG ta cimma matsaya da kamfanin DangoteƘungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a NajeriyaEl-Rufa'i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi'Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jiharKofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPPBurkina Faso ta amince da dokar haramta neman maza a faɗin ƙasarAn bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan SatumbaGwamnatin Najeriya ta yi maraba da ɗaure Simon Ekpa a FinlandAtiku ya nemi a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin RiversAn yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a Finland
X whatsapp