Wasu mahara da ake zargin ‘Yan Bindiga ne sun yi awon gaba da wani matashi mai kimanin shekaru 18 da haihuwa mai suna Victor Egbon a unguwar Zone A dake yankin Kuje a birnin tarayya Abuja, bayan sun raunata mahaifinsa.
Victor da ne ga mamallakin makarantar Supreme Kids Academy, dake birnin tarayyar Nijeriya.
Read Also:
An rawaito cewa an garzaya da mahaifin matashin mai suna Abdulsalam Ozigi asibiti sakamakon mugun raunin da ‘yan ta’addar suka ji masa a jikin shi.
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakayi sunan sa, yace ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Ozigi da misalin karfe 12:15 na daren litinin, inda suka yi awon gaba da Victor bayan sun lalata wasu kofofin gidan.