Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Binne Ma’aikacin Poly Bayan Sun Karbi Miliyan 4

‘Yan Bindiga Sun Binne Ma’aikacin Poly Bayan Sun Karbi Miliyan 4

‘Yan bindiga sun hallaka ma’aikacin makarantar Polytechnic ta Talata-Mafara a jihar Zamfara Sanusi Halliru bayan sun karbi kudin fansar sa Naira miliyan 4.

‘Yan ta’addan sun yi garkuwa dashi ne akan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda yake kokarin zuwa wajen wani taron karawa juna sani kafin yiwa kasa hidima.

Sun bukaci a biya naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa, sai dai ba’a biya su kudin akan lokacin ba hakan ta sanya su halaka shi tare da binne gawar a cikin daji,

Wani makusanci mamacin, Muhammad Nasir, yace bayan sun tara miliyan Hudun sun kira ‘yan bindigar domin su fadi inda zasu kawo musu kudin su fanshi dan uwan su.

“Shugaban ‘yan bindigar ya fada mana lokaci da kuma wanda zai zo domin karbar kudin”. Amm da muka isa wajen bamu iske kowa ba.

“Sai daga bisani muka hangi wasu mutane saman Babura, da zuwan su suka bukaci mu basu kudin.

“Mun kuma mmika kudin gare su, said ai guda cikin su yace mana tuni dan uwan mu ya mutu.

“Mun bukaci su bamu gawar domin yi masa sutura kamar yadda Addini ya tanada, amma ga mamakin mu sai suka ce ai ya dade da mutuwa don haka sun binne shi.

“Sannan suka juya hankali kwance suka koma inda suka fito, Nasir ya bayyana hakan cikin bakin ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp