Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong ya nemi afuwar mabiyan mabiya darikar Katolika kan kalamansa da suka jawo ce-ce-ku-ce lokacin da ya ke kare matsayar nadin da jam’iyyarsa ta APC ta yi ma sa.
Tun a ranar Talata aka soma wata takaddama tsakanin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong da Mabiya addinin Kirista ‘yan darikar.
Read Also:
Hakan ya biyo bayan kalaman da gwamnan ya yi cewa Fafaroma Francis bai ga laifin karbar mukamin darakta-janar na kamfe din dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, ba duk da cewa dukkansu Musulmai ne.
Kalaman sun fusata kiristoci mabiya katolika wadanda suka bayyana ambato sunan Fafaroma a matsayin raini ga jagoran nasu.
Abin da ya kai ga sun bukaci a gaggauta dakatar da Lalong daga harkokin cocin.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa cocin, Lalong ya amsa cewa ya yi kuskure don haka ya nemi a yafe ma sa, da alkawarta ci gaba da ayyukansa ta hanya mafi dacewa.
Gwamna Lalong ya ce bai yi wadannan kalamai ba domin muzanta kiristocin kasar.